(ABNA24.com) Sojojin Siriya sun samu nasarar shiga garin Khan Shayhum na kudancin lardin Idlib, yankin da ke muhimmanci ta fuskar dubarun yaki.
Tashar Talabijin din Al-alam dake ta ruwaito cewa a ci gaba da tsarkake kasar daga 'yan ta'adda, dakarun tsaron Siriya sun samu nasarar tsarkake kauyen Midaya da tsaunukan dake kewayen garin Khan Shaykhun tare da kutsawa cikin garin.
Dakarun tsaron Siriya sun yi amfani da manyan makaman yaki akan 'yan ta'adda tare da tsarkake tsaunukan Annar da ke kewaye da garin na Khan Shaykhun.
A bangare guda jiragen yakin Rasha da Siriya sun yi luguden wuta kan maboyar 'yan ta'addar Annusra a garuruwan Khan Shaykhun da Rikaya da Shekh Mustapha tare rusa sansanonin 'yan ta'adda da kuma hanyoyin kai musu dauki.
Garin Khan Shayhun, yanki ne mai matukar muhimmanci ta fuskar, kuma tsarkake shi na a matsayin matakin farko na bude hanyar da ta hada lardin Aleppo da birnin Damascus.
/129
19 Agusta 2019 - 07:06
Lambar labari: 969952
Sojojin Siriya sun samu nasarar shiga garin Khan Shayhum na kudancin lardin Idlib, yankin da ke muhimmanci ta fuskar dubarun yaki.